IQNA

An Bukaci A Kafa Kwamitin Binciken Gaskiya Kan Kisan 'Yan Shi'a

9:32 - January 03, 2016
Lambar Labari: 3480016
Bangaren kasa da kasa, a lokacin da wasu mambobi a harkar muslunci a Najeriya suka gana da wasu yan majalisar dokokin kasar sun bukaci da a kafa kwamiti wanda zai yi binciken gaskiya kan kisan 'yan shi'a.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Ahlul bait cewa, wasu daga cikin mambobin harkar muslunci a Najeriya sun gana da wasu daga cikin yan majalisar dokokin najeriya, inda suka bukaci cewa dole ne a kafa kwamiti wanda zai bi kadun abin da ya faru, kan kisan yan shia da kuma kame sheikh Ibrahim zakzaky.
Bayanin ya ci gaba da cewa tun bayan kai harin da sojojin Najeriya suka yi a kan mabiya mazhabar shi'a tare da kashe adadi mai yawa na mabiya mazhabar shi'a karkashin jagorancin malamin da kuma almajiransa.
A kwanakin baya ne dakarun sojin Najeriya suka kai hari kan Husainiyyar Bakiyyatullah da ke birnin zaria ta mabiya mazhabar shi'a, inda suka kasha wasu daga cikinsu, kamar yadda kuma suka kai wani harin a gidan sheikh Zakzaky, tare da kasha dukaknin mutanen da suka samu a gidansa tare da kame shi.
Har yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta bayar da wani bayani takamamai kan dalilin yin wanan kisa na daruruwan fararen hula da bas u dauke da makamai ba, illa dai kawai suna bayar da hujjar cewa an tare hanyar shugaban sojoji nea  lokacin da yake wucewa.
3471677
captcha