IQNA

Hakika Bayina Na Gari Ne Za Su Gaji Kasa

وَلَقَد كَتَبنا فِي الزَّبورِ مِن بَعدِ الذِّكرِ أَنَّ الأَرضَ يَرِثُها عِبادِيَ الصّالِحونَ
Hakika Mun Rubuta A Cikin Zabura Bayan Zikr (Attaura) cewa, Hakika Bayina Na Gari Ne Za Su Gaji Kasa.
(Suratul Anbiya) 105


‘Yan adam suna ganin yadda masu wuce gona da iri sukeyin zalunci suna danne hakkokin mutane, kada su zaton cewa karshen lamarin kenan, kada su tsammanin cewa daga karshe babu wata mafita; ba haka lamarin yake ba, su sani cewa wannan yanayin mai wucewa ne wannan yana da dangantaka ne da wannan duniyar kuma dabi’ar wannan duniyar ce haka,  ko shakka babu gaskiya da adalci za su kafu kuma za su yi iko a bayan kasa.
Ayatollah Khamenei  20-9-2005

Abin da ya kamata ya zama cikin kwakwalen ‘yan adam a yau shi ne, su sani su yi yakini kan cewa, wani mutum mai madaukakin matsayi na zuwa, zai tseratar da duniya daga zalunci da danniya; Wannan shi ne abin dukkanin annabawan Allah suka yi kokari a kansa,  shi ne kuma abin da manzon mulsunci a cikin wata aya yya yi alkawali a kansa, (ya cire kukumi da sarkokin da ke kansu)   Suratul A’araf: 157
Ayatollah Khamenei 23-11-2008

Duk da irin barazanar da masu girman kai suke yi da hankoro ta fuskar kudi, soji, siyasa, da tsaro, masu girman kai da masu yi musu amshan shata domin ci gaban zalincinsu a yankin gabas ta tsakiya da sauran yankunan duniya musulmi, duk da hakan tabbas, lokaci mai zuwa yana damfare ne da addinin muslunci.
Ayatollah Khamenei  17-8-2015