IQNA

Zanga-Zangar Adawa Da Kudirin Trump A Los Angeles

23:42 - October 15, 2017
Lambar Labari: 3482003
Bangaren kasa da kasa, cincirindon Amurka ne suka gudanar da wani gangamia yau a garin Los ngele na Amurka domin nuna adawa da shirin Trumpna korar baki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Los Angele Times ta bayar da rahoton cewa, masu gangamin sun hada da musulmi da wadanmda ba musulmi ba, karkashin wani kamfe mai taken (#NoMuslimBanEver).

Wannan kamfe dai yana nuni da cewa Amurkawa basu yarda da shirin Trump na kyamar msuulmi ba tare da haramta musu hakkokinsu ko kuma hana su shiga cikin Amurka.

Masu gangamin sun bukaci mahukunta musaman a bangaren shari’a da su zama masu ‘yanci ba ‘yan amshin shata ga masu mulki ba, domin kuwa dukkanin abin da Trump yake na nuna kyama ga musulmi ya sabawa tsarin doka a Amurka, wanda ya kamata ya fuskanci hkunci a kan hakan.

Tun kafin Trump ya dare kan shugabancin Amurka, yay I ta yin kamalan batunci ga addinin muslunci da musulmi tare da shan alwashin zai shiga kafar wando daya da musulmi da yake kiransu ‘yan ta’adda.

Duk kuwa da cewa bayan hawansa ya karbi cin hanci daga wasu kasashen larabawa masu daukar nauyin akidar ta’addanci a duniya wadanda ya ce zai yanke alakar Amurka da su, inda yanzu su ne manyan abokan kawancesa a gabas ta tsakiya, inda su kuma suke ta mika masa daruruwan biliyoyin daloli namna fetur da suke sayarwa.

3652737


captcha