IQNA

A Karon Farko Za A Gudanar Da Baje Kolin Kayan Mata Musulmi A San Francisco

20:21 - January 16, 2018
Lambar Labari: 3482305
Bangaren kasa da kasa, a  karon farko za  agudanar da wani baje kolin kayan mata musulmi a birnin San rancisco na kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na digitaljournal ewa, a cikin satumban wannan shekara ta 2018 a  karon farko za  agudanar da wani baje kolin kayan mata musulmi a birnin San rancisco da ma wasu birane na duniya.

A wannnan baje koli za a nuna kayan mata musulmi da suke yin amfani da su cikin sauki, wadanda za a iya yin amfani da su a koina tare da rufe jiki kamar yadda yakea musulunci.

Said Laura Camerlengo ita ce mai kula da baje kolin tufafi a birnin, ta bayyana cewa hakika gudanar da wannan baje koli na tufafin musulunci na mata yana da matukar muhimmanci, domin mutane da dama za su kara samun masaniya kan tufafin musulmi.

Kuma wannan zai kara wayar da kan mutane su gane cewa tufafin musulmi ba abin kyama ba ne, kaya na kwalliya kamar sauran kaya, sai dai tsari ne kawai ya banbanta.

3682548

 

 

 

captcha