IQNA

An Bude Taron Taimakon Qudus A Birnin Alkahira

22:21 - January 17, 2018
Lambar Labari: 3482307
Bangaren kasa da kasa, an bude babban taro na kasa da kasa mai taken taimakon Qudus a birnin Alkahira na kasar Masar wanda shugaban kasar Abdulfattah Sisi da cibiyar Azhar suke jagoranta, tare da halartar wakilan kasashe 86 na duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau Laraba ce shugaban Jami'ar Al-Azhar ta kasar Masar Sheikh Ahmad Al-Tayyib ya bude wani taron kasa da kasa na nuna goyon baya ga birnin Kudus da Masallacin Al-Aqsa a birnin Alkahira, babban birnin kasar ta Masar don tattauna hanyoyin da za a bi wajen ba da kariya ga birnin na Kudus daga barazanar da yake fuskanta.

A safiyar yau Laraba ce Sheik Ahmad al-Tayyib, shugaban jami'ar ta Al-Azhar ya bude wannan taron na kwanaki biyu wanda ya sami halartar manyan jami'an kasar ta Masar da kuma wakilan kasashe sama da tamanin na musulmi da na larabawa.

A jawabin da ya gabatar wajen bude taron, Sheikh al-Tayyib ya kirayi kasashe musulmi da na larabawa da ya kyam wajen fada da matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na sanar da Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila, yana mai cewa ko ba dade ko ba jima sai an kawar da haramtacciyar kasar Isra'ila 'yar mamaya.

Shi ma a nasa jawabin shugaban gwamnatin cin gashin kan Palastinawa Mahmud Abbas Abu Mazin ya sake jaddada matsayarsa na kin amincewa da Amurka a matsayin mai shiga tsakani cikin tattaunawar sulhu tsakaninsa da sahyoniyawan yana cewa zabi ya rage wa shugaban Amurkan kan wannan matsaya da ya dauka.

3682966

 

captcha