IQNA

Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kai Hari A Kamaru

22:23 - January 17, 2018
Lambar Labari: 3482308
Bangaren kasa da kasa, bayan harin da ‘yan ta’addan Boko haram suka kai kan wani masallaci sun kuma kasha mutane biyu a yankin far North Region.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Majiyar tsaron Kamaru ta sanar da cewa, 'Yan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram sun kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kauyuka uku da suke shiyar arewacin kasar.

Majiyar tsaron Kamaru ta sanar da cewa: 'Yan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kauyuka uku da suke shiyar arewacin kasar, inda suka kona gidajen jama'a kimanin dari tare da janyo hasarar rayukan mutane akalla hudu.

Tun bayan bullar masifar kungiyar Boko Haram a shekara ta dubu biyu da tara a shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya, masifar ta kutsa har cikin kasashen da suke makobtaka da Nigeriya da suka hada da Jamhuriyar Niger, Kamaru da Chadi, kuma mutane fiye da dubu ashirin ne suka rasa rayukansu yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka tsere daga muhallinsu.

3683088  

 

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha