IQNA

Musulmin Malta Na Jiran Izini Daga Gwamnati Domin Gina Masallaci

23:13 - January 18, 2018
1
Lambar Labari: 3482309
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Malta na jiran samun izini daga gwamnatin kasar domin gina masallacin da za su rika yin salla.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na timesofmalta cewa, Badar Zaina daya ne daga cikin mambobin kwamitin musulmi na kasar Malta yana bayyana cewa, tun kimanin shekaru 18 da suka gabata suka rubuta wasika ga gwamnati suna neman a basu damar gina masallatai da za su rika yin salla, amma har yanzu ba a ba su izini ba.

Yace tun a lokacin sun tara kudinsu domin gudanar da wannan aiki, amma gwamnati ta yi biris da batun, inda a cikin 2015 suka samu wani babban gini da suke yin salla a ciki a garin Msida, shi ma gwamnati ta hana su yanzu.

Tibirin Malta yana cikin Bahrum, kuma awai mutane kimanin dubu 400 da suke rayuwa a cikinsa, kimanin 6000 musulmi ne, amma ana haramta musu gudanar da ayyukan ibada  acikin ‘yanci, inda masallaci daya ne ske da shi a fadin tsibirin, wanda shi ma tun a cikin 1978 aka gina shi.

3683071

 

 

 

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
LAWALI MUSA MOREWA
0
0
KAMATA YAYI MUSULMIN DUNIYA SUSA BAKI A SIYASANCE, DON SUSAMU Y'ANCI.
captcha