IQNA

Jin Ra’ayin Jama’a Kan Saka Hijabi A Wata Makaranta A Ingila

23:19 - January 18, 2018
Lambar Labari: 3482311
Bangaren kasa da kasa, an saka wani jin ra’ayin jama’a dangae da hana saka hijabi a wata makaranta da ke yankin Newham a birnin London na kasar Birtaniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Newham Recorder cewa, makarantar Saint Steven da ke cikin birnin London ta kafa dokar hana dalibai mata kasa da shekaru 8 saka hijabi a cikin makarantar ko yi azumi.

Mafi yawan daliban da suke a wannan makaranta dai ‘yan asalin kasashen India, Pakistan da kuma Bangaladesh ne.

Nina Lal day ace daga cikin malaman wannan makaranta, kuma ‘yar asalin kasar India, ta bukaci hukumomin makarantar da su janye dokar hana dalibai saka hijabin muslunci, domin iyayen yara musulmi suna kokawa da wannan doka.

Wannan ne ya sanya ta saka wani jin ra’ayin jama’a a kan wannan doka a shafinta na yanar gizo, inda ya zuwa yanzu fiye da mutane duu takwas suka bukaci a janye wanan doka.

Wannan dai bas hi ne karon farko da ae fuskatar irin wannan matsala a makarantun kaar Birtaniya ba, inda wasu daga cikinsu musamman ma masu zaman kansu, sukan hana dalibai mata saka hijabin musluncia  cikin makarantun, lamarin da ke cutar da musulmi matuka

3683114

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha