IQNA

Taron Bahasi Kan Masihu A Cikin Kur'ani A Connecticut

22:51 - January 20, 2018
Lambar Labari: 3482318
Bangaren kasa da kasa, a gobe ne za a fara gudanar da wani zaman taro mai taken Isa Masihua  cikin kur'ani mai tsarki a jahar Connecticut ta kasar Amurka.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Ridgefield Press cewa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro mai taken Isa Masihua  cikin kur'ani mai tsarki a jahar Connecticut ta kasar Amurka domin wayar da kan mabiya addinai.

Bayanin ya ce babbar manufar gudanar da wannan zama ita ce karawa juna sani da kuma wayar da kai kan matsayin annbi Isa (AS) a cikin addinin muslunci.

An ambaci sunayen annibi  Isa (AS) da kuma Maryam (AS) a wurare daban-daban cikin kur'ani mai tsarki.

Sunan annibi Isa (AS) ya zo har sau 25 a cikin kur'ani mai tsarki, tare da bayyan shi a matsayin Kalmar Allah, wanda Allah ya turo shi domin shiryar da dana dam da kuma ceto sh daga bata zuwa shiriya daga duhu zuwa haske.

3683490

 

 

 

captcha