IQNA

Limamin Tehran: Harin Da Aka Kaiwa Syria Alama Ce Ta Dabbanci A Cikin Lamarin Amurka

23:47 - April 20, 2018
Lambar Labari: 3482588
Bangaren siyasa, Wanda ya jagoranci sallar Juma'a a Tehran ya bayyana cewa, harin da Amurka ta jagoranci wasu suka kaddamar a kan Syria, wata babbar alama ce kan yadda Amurka take yin watsi da dokokin kasa da kasa, tare da yin gaban kanta wajen aiwatar da siyasarta ta ina da yaki a duniya.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarat cewa, Hojjatol Islam Sheikh Kazem Siddiqi a yayin da yake gabatar da hudubar Jum'a a yau a birnin Tehran na kasar Iran ya bayyana cewa, babban abin da yake a gaban Amurka shi ne ta yi amfani da karfi wajen aiwatar da siyasarta.

Ya ce abin da ya faru a Syria sabanin abin da maharan suke bayyana wa duniya ne, domin kuwa sun kaiwa Syria hari ne sakamakon gazawar 'yan ta'adda da suka kasa aiwatar musu da wannan aikin tsawon shekaru, shi ne a halin yanzu suka karbi ragamar kai hare-haren da kansu.

Dangane da shirin Trump na dauke ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa birnin Quds mai alfarma kuwa, malamin ya bayyana hakan a matsayin wani matakin tsokana ga dukkanin musulmi na duniya, da kuma neman shafe taswirar palastinu daga doron kasa.

Dangane da kisan kiyashin da Isra'ila take yi kan al'ummar palastinu tare da cikakken goyon bayan Amurka kuwa, sheikh Siddiqi ya bayyana cewa, zaluncin Isra'ila maras misiltuwa, shi ne zai gagauta kawon karshenta.

haka nan kuam malamin ya yi Allawadai da yadda wasu daga cikin sarakunan larabawa suka zama 'yan amshin shata a kan dukkanin abin da Amurka da yahudawa suke bukata, inda ake yin amfani da su domin rusa kasashen musulmi da ma na larabawa tare da su da biliyoyin kudadensu.

3707230

 

 

 

 

 

captcha