IQNA

Shugaban Jam’iyyar Labour A Birtaniya Ya Jinjinawa Majalisar Musulmin Kasar

23:47 - April 22, 2018
Lambar Labari: 3482592
Bangaren kasa da kasa, Shugaban jam’iyyar Labour a kasar Birtaniya ya jinjinawa majalisar musulmin kasar kan kokarinta na samar da fahimtar juna.

 

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya habarta cewa, Jeremy Corbyn shugaban jam’iyyar Labour a Birtaniya ya yaba wa majalisar musulmin kasar, kan ayyukan da ta gudanar tsawon shekaru.

Corbyn ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron da majalisar ta shirya domin cika shekaru 20 da kafa ta, inda ya bayyana a cikin wadannan shekaru ashirin, majalisar ta taka rawar gani, wajen wayar da kan mutane da yada zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.

Baya ga Jeremy Corbyn akwai wasu daga cikin ‘yan siyasa da suka hada da ‘yan majalisar dokokin Birtaniya da suka halrci wurin taron.

Wannan cibiya dai ta gudanar da ayyuka masu yawa a cikin shekaru ashirin da kafata, da hakan ya hada har da gina masallatai fiye da 200a  cikin kasar.

An kafa majalisar ne dai tun a cikin shekara ta 1997, domin kare hakkokin musulmin kasar Birtaniya.

3707407

 

 

 

 

captcha