IQNA

Yarjeniya A Bangaren Bunkasa Ilimi Da Bincike Tsakanin Iran Da Kenya

23:52 - April 24, 2018
Lambar Labari: 3482600
Bangaren kasa da kasa, an rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ke nufin kara bunkasa harkokin ilimi da bincike tsakanin Iran da Kenya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren hulda da jama’a na cibiyar bunkasa harkokin ilimi da a’adu ta kasar Iran ya sanar da cewa, karamin ofishin jakadancin Iran da ke kasar Kenya ne ya jagoranci tawagar Iran wajen rattaba hannu kan wannan yarjejeniya a kasar ta Kenya.

An rattaba hannu kan wannan yarjejeniya tsakanin kasashen Kenya da Iran ne a jami’ar Pwani, kuma yarjejeniyar kunshi yin aiki na hadin gwiwa ta fuskar bincike a kan harkokin addinai da tarihi.

Haka nan kuma a cikin yarjejeniyar an cimma matsaya kan cewa, daliban kasar Kenya da suke karatun harshen farisanci za su samu guraben karatu kyauta a jami’oin kasar Iran.

Haka nan kuma za a rika shirya tarukan karawa juna sani a kan wasu muhimman lamurra da suka shafi bincike na ilimi a kan lamura da za su amfanar da kasashen biyu.

3708343

 

 

 

 

 

captcha