Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mir'at Bahrain cewa, a jiya ne jami'an tsaron masarautar kama karya ta Bharain sun kame Hajj Hassan Khamis Nu'aimi, saboda ya yi baitocin waka na yabon Imam Hussain(AS) da kuma nuna sha'awarsa ta ziyartar Karbala.
An kame wannan mutum ne bayan da wata 'yar koren masarautar kama karya ta Bahrain Susan Sha'ir ta rubuta a jaridar Watan cewa, kalaman da ya yin a son ziyartar karbala kalamai ne na rashin kishin kasarsa, inda yake son wata kasa fiye da kasarsa.
Bayan rubuta wannan Makala ne jami'an tsaro suka dira a gidansa suka yi awon gaba da shi a gaban iyalansa.