IQNA

Baje Kolin Kayan Fasahar Iran A Fagen Rubutun Ayoyin Kur'ani A Girka

23:42 - April 26, 2018
Lambar Labari: 3482606
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani baje kolin nuna fasahar marubutan kur'ani na kasar a Kasar Girka.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al'adun muslunci cewa, an fara gudanar da baje kolin kayan fasahar rubutun ayoyin kur'ani na wasu daga cikin marubuta Iraniyawa a kasar Girka.

Daga cikin fitattun masu fasahar rubutun da suka halarci har da Mujtaba Sabzeh da kuma Fatima Kikawusi, wadanda dukkanin fitattun masu fasahar rubutun ayoyin kur'ani a kasar Iran.

Wannan baje koli da aka fara gudanar a jiya Laraba, zai ci gaba har zuwa wasu kwanaki a nan gaba, inda mutane suke ci gaba da halartar wurin domin duba irin wannan fasaha ta rubutun ayoyin kur'ani da salo daban-daban.

3708950

 

captcha