IQNA

Kafa Cibiyar Bincike Kan Ilmomin Musulunci A Kasar Faransa

23:44 - April 26, 2018
Lambar Labari: 3482607
Bangaren kasa da kasa, jami'ar Marmara ta kasar Turkiya na shirin gina wata bababr cibiyar bincike kan ilmomin addinin musulunci a birnin Strasbourg na kasar Faransa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na TRT Haber cewa, jami'ar Marmara ta kasar Turkiya na shirin gina wata bababr cibiyar bincike kan ilmomin addinin musulunci a birnin Strasbourg na kasar Faransa nan ba da jimawa ba.

Wannan cibiyar dai za ta mayar da hankali wajen bayar da dama ga masu bincike kan lamurra da suka shafi akidar musulunci da kuma yadda muslunci yake a ilmance.

Haka nan kuma cibiyar za ta bayar da dama ga musulmi da ma wadanda ba musulmi domin su samu gudanar da bincike a cikin 'yanci, tare da samar da dukkanin abin da abukata domin gudanar da bincken.

3709378

 

captcha