IQNA

Sabuwar Cibiyar Horar Da Mata Hardar Kur’ani A Libya

23:35 - July 09, 2018
Lambar Labari: 3482820
Bangaren kasa da kasa, an bude wata sabuwar cibiyar horar da mata hardar kur’ani mai tsarki a kasar Libya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka bude wata sabuwar cibiyar horar da mata hardar kur’ani mai tsarki a kasar Libya a yankin Jalo na kasar.

Bayanin ya kara da cewa, wannan cibiya za ta mayar da hankali ne wajen bayar da horo kan hardar kur’ani ga mata zalla.

An dai dauki tsawon shekaru hudu ana gina wannan cibiyar wadda ta hada azuzuwan koyarwa da kuma wuraren hutawa gami da masallaci da dakin taro, da dai sauraren wuraren da ake bukata.

Haka nan kuma an gina wurin ne da hawa biyu, wanda za a yi amfani da hawa na farko domin ayyukan ofishin da sauransu, hawa na biyu kuma a matsayin azuzuwan karatu.

3728718

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha