Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na IPP ya habarta cewa, Sheikh Afifi ya kasance daya daga cikin manyan limamai na kasar Australia, kuma a cikin watan Maris na wannan shekara aka zabe shi a matsayin babban mai bada fatawa ga musulmi na kasar.
Babbar majalisar muuslmin kasar Australia ta fitar da sanarwar taaziyya ga dukkanin musulmin kasar kan wannan babban rashi.
A cikin bayanin an bayyana shi matsayin mutumin da ya kwashe fiye da shekaru 20 yana hidima ga muuslmin kasar.
Robbin Scott ministan al’adu na kasar Australia ma ya fitar da bayanin ta’aziyya kan rashuwar sheikh Afifi.
Akwai muuslmi kimanin dubu 600a kasar Australia, wato kimanin kashi 3 cikin dari na dukkanin al’ummar kasar.