IQNA

Harin Bam Ya Kashe Mutane 85 A Wani Gangamin Siyasa A Pakistan

23:46 - July 13, 2018
Lambar Labari: 3482833
Bangaren kasa da kasa, Rahotanni daga kasar Pakistan sun ce akalla mutane 85 sun rasa rayukansu a wani harin bam da aka kai a kan wani gangamin zabe a yankin Balochestan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an kai harin ban din ne a yau Juma'a,a lokacin da jama'a masu tarin yawa suka hadua wani gangamin yakin neman zabe a garin Mastung da ke kusa da birnin Kuita babban birnin lardin Balochestan.

Akalla mutane 85 sun rasa rayukansu, wasu fiye da 150 kuma sun jikkata, daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da wasu fitattun 'yan siyasa na lardin da suka hada da Mir Siraj.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, amma dai ana nuna yatsan tuhuma a kan kungiyar Taliban da kungiyoyin masu dauke da akidun takfir.

3729634

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha