IQNA

Baki Na Ci Gaba Da Isa Karbala Domin Halartar Tarukan Ashura

23:31 - September 19, 2018
Lambar Labari: 3482994
Bangaren kasa da kasa, mahukunta a birnin karbala na kasar raki sun sanar da cewa sun kammala dukkanin shirye-shirye domin daukar nauyin bakuncin tarukan Ashura.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Majid Maliki mamba na majalisar lardin Karbala ya fadi a gaban manema labarai cewa, an kammala dukkanin shirye-shirye domin daukar nauyin bakuncin tarukan Ashura da za a gudanar a goe idan Allah ya kai mu a hubbaren Imam Hussain (AS) da Abbas (AS).

Ya ci gaba da cewa shirin ya hada da bangaren tsaro, inda yanzu haka jami’an tsaro dubu talatin ne a cikin kayan sarki aka rarraba su a koi’ina a cikida wajen birnin na krabala, baya ga jami’an tsaro na farin kaya da suke a cikin jama’a.

Maliki ya ce manufar hakan ita ce tabbatar da cewa an bayar da kariya ga jama’a masu halatar wadannan taruka daga suka zo daga sasan Iraki da kuma kasashen duniya, domin ziyartar Imam Hussain (AS).

A gobe ne za a gudanar da tarukan Ashura domin tunawa da zagayoar ranar shahadar Imam Hussain (AS) da iyalan gidan amnzo da suke tare da shi.

3748422

 

 

 

 

captcha