Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, sakamakon hare-haren ta’addancin da makiya mazhabar ahlul bait (AS) suke kai wa kan tarukan Ashura a wurare daban-daban a kasa Afghanistan, wannan ya sanya a wannan shekara gwamnatin kasar ta dauki kwarar matakai na tsaro domin bayar da kariya ga masu gudanar da wadannan taruka.
A cikin shekarun baya-bayan nan tun daga lokacin kafa kungiyoyin ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi da suke kashe muuslmi a kasashe daban-daban da sunan jihadi, irin wadannan ‘yan ta’adda masu dauke da akidar wahabiyanci sun sha kai hare-haren bama-bamai a kan masallatai da cibiyoyin addini a lokacin da mabiya mazhabar shi’ar ahlul bait suke gudanar da tarukansu musamman ma na Ashura.
A wannan karon an tura daruruwa jai’an tsar da kayan aiki a dukkanin warren da ae gudana da arukan ashura a kasar Afghanistan, domin hana ‘yan ta’adda kai musu hare-hare.