IQNA

Soyayyar Imam Hussain (AS) Ta Hada Kan Musulmi A Ghana

22:53 - September 22, 2018
Lambar Labari: 3483003
Bangaren kasa da kasa, sakamakon soyayyar da musulmi suke yi wa Imam Hussain (AS) wannan ya hada su a wuri guda a Ghana.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin gudanar da tarukan Ashura, musulmi masu mabanbantan ra'ayoyi sun hadu wuri guda domin juyayin shahadar Imam Hussain (AS) a kasar Ghana.

Bayanin y ace jami'ar Almostafa ta dauki nauyin shirya taron Ashura domin juyayin shahadar Imam Hussain (AS) da iyalan gidan manzon Allah (SAW) kuma taron ya samu halartar dukkanin bangarori na musulmin kasar.

Baya ga malaman mabiya mazhabar shi'ar Ahlul bait (AS) wasu daga cikin malaman Sunnah musamman bangaren mabiya dariku sun halarci wurin, inda wasu daga cikinsu ma suka gabatar da jawabai kan matsayin Imam Husain (AS) da kuma iyalan gidan manzon Allah (SAW) da kuma zaluncin da aka yi musu bayan rasuwar manzo.

Haka nan kuma an karanta kasidu na tunatarwa kan abin da ya faru a Karbala a ranar Ashura, da kuma fitar da darussan da wannan lamari yake koyar da al'ummar musulmi dama 'yan adam baki daya.

3748760

 

 

 

 

 

captcha