IQNA

Ci Gaba Da Tarukan Da Suka Danganci Ashura A Ghana

23:55 - September 23, 2018
Lambar Labari: 3483005
Bangaren kasa da kasa, Bayan tarukan Ashura da aka gudanar a ranakun tara da kuma goma ga Muharram a Ghana, a jiya Asabar dubban mabiya mazhabar shi’a sun gudanar da wani taron kan ribatattun Karbala a birnin Accra.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, dimbin mabiya mazhabar shi’ar sun gudanar da jerin gwano a cikin unguwannin da musulmi suke da zama a cikin birnin Accara fadar mulkin kasar Ghana.

Daga bisani kuma an kammala taron a babban filin wasanni na Kutubabi Accra, inda aka nuna yadda aka yi wa mata da kanan yara daga cikin iyalan gidan manzon Allah da suke tare da Imam Hussain (AS) bayan kisan gillar da aka yi masa da ‘ya’yansa maza da kuma sahabbansa.

Ya zo a cikin tarihi cewa, daga matan da aka kame amatsayin ribatattun yaki har da Zainab diyar Fatima ‘yar manzon Allah (SAW) wadda aka ci zarafinta tare da sauran mata da yara daga cikin zuriyar manzon Allah wadanda suka yi saura a lokacin.

An daure su da sarkoki daga Karba da ake cikin Iraki har zuwa birnin Damascus na Syria wanda shi ne fadar Yazidu a lokacin.

Sheikh Abubakar Kamalulldin shugaban ‘yan shi’a na Ghana ya ce; dalilin gudanar da wannan jerin gwano shi ne domin a nuna wa jama’a abin da ya faru a aikace, wanda ake karantawa a tarihi ana wucewa.

An gudanar da irin wadannan taruka na Ashura a kasashen Afrika da dama, kamar yadda kuma a Najeriya ma an gudanar da irin wannan gagarumin taro da kuma jerin gwano a ranakun Tasu’a da Ashura a birane daban-daban na kasar.

3749147

 

 

 

captcha