IQNA

A Zirin Gaza Ma'aikatan UNRWA Sun Shiga Yajin Aiki

23:54 - September 24, 2018
Lambar Labari: 3483011
Bangaren kasa da kasa, Ma’aikatan cibiyar bayar da agaji ga ‘yan gudun hijira Falastinawa UNRWA sun shiga yajin aiki a dukkanin yankunan zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna, mataimakiyar shugaban gamayyar ma’aikatan cibiyar ta UNRWA a Gaza Amal Batash ta bayyana cewa, sun dauki wannan matakin ne domin nuna rashin dadinsu dangane da ayyukan cibiyar suke ci gaba da kara sakwarkwacewa.

Ta ce a halin yanzu akwai albashin ma’aikatan cibiyar wadanda suka dogara da domin hidimominsuna yau kullum, amma an shiga wata na biyu ba tare da sun samu albashin watan da ya gabata ba.

UNRWA dai ita ce cibiyar da ke karkashin majalisar dinkin duniya, wadda take gudanar da ayyukan tallafa wa Falastinawa ‘yan gudun hijira a ciki da wajen Palastine.

Daga cikin ayyukan kungiyar hard a samar da makarantu da kuma asibitoci da magunguna har ma da abinci ga miliyoyin Falastinawa da Isra’ila ta kora daga yankunansu.

Yanzu haka dai cibiyar tana da amnyan ofisoshinta ne a Zirin Gaza, Ramallah, da kuma kasashen Lebanon, Jordan da kuma Syria.

3749605

 

captcha