IQNA

Dalibai Dubu 100 Sun Yi Rijista A Makarantun Kur'ani A Aljeriya

22:37 - November 08, 2018
Lambar Labari: 3483111
Bangaren kasa da kasa, dalibai fiye da dubu 100 sun yi rijista a makarantun kur'ani mai tsarki a birnin Aljiers fadar mulkin Aljeriya.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, Zuhair Buzera babban daraktan ma'aikatar kula da harkokin addini a birnin Aljiers fadar mulkin Aljeriya ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu daliabi fiye da dubu 100 ne suka yi rijistar sunayensu a makarantun kur'ani mai tsarki a birnin na Aljiers.

Ya ce daga cikin daliban kimanin dubu 45 sun yi rijistar ne a bangaren karatun kur'ani zalla, yayin da sauran kuma sun yi rijistar nea  bangaren karatun book da na addini.

Makarantun kur'ani a Aljeriya dai ana koyar da ilmomi na zama baya ga kur'ani, inda kuma ake la'akari da shedar kamala karatu a wanna makarantu.

Ya kara da cewa yanzu haka za a bude wasu makarantun kur'ani 3, wadanda kowanne za ta dauki dalibai 1200

3762242

 

captcha