IQNA

An Saka Wani Dadadden Kur’ani A Kasuwa Wanda Aka Tarjama Da Ingilishi

23:56 - December 06, 2018
Lambar Labari: 3483187
Bangaren kasa da kasa, an saka wani kwafin kur’ani da aka tarjama tsawon daruruwan shekaru da suka gabata a cikin harshenturanci a kasuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin da ke saka kayan tarihi domin tallarsu a yanar gizo Jelly Fish Tree ya sanar da cewa, an sanya wannan kwafin kur’ani da aka tarjama a shekarar 1649 a kasuwa domin fansar da shi.

Wannan shafi dai na kasar Afirka ta kudu ne, kuma yak an saka tallar abubuwa masu kima da tarihi ne kawai domin sayar da su.

Yanzu haka dai kima ta farko da aka sanya wa wannan kur’ani shi ne dala dubu 800.

3770019

 

 

 

 

captcha