Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na DMCA ya bayar da rahoton cewa, a jiya Asabar ne aka bude taron babbar gasar kur’ani ta duniya karo na 16 a jami’ar Malik Bin Anas a birnin Qartaj na kasar Tunisia , mai taken Allah bin Arafah, wadda ministan harkokin adini na kasa Ahamd Azum ya jagoranci budewa.
Ahamd Al-sawafi daga Oman da Amir Amushri daga Aljeriya, da Aus Al-Utaibi daga Jorda, sai kuma Hamd Al-hashash daga Bahrain, su ne suka fara gudana da karu a ranar farko ta gasar.
A bayanin da ya gabatar a wajen bude gasar, Aham Naufal daga ma’aikatar kula da harkokin addinia Tunisia ya bayyana cewa, a wannan karon an kara bangaren tafsirin kur’ani a cikin bangarorin gasar.
Kasashe da dama ne suke halartar gasar, da suka hada da Aljeriya, Iran, Saudiyyah, Mauritaniya, Libya, Masar, Jordan, Oman, Qatar, Palastine, Russia, Sudan, Kuwait, UAE, Bahrain, Malaysia, Indonesia, Iraki, Lebanon da sauransu.