Kamfanin dillancin labaran iqna, tun a jiya ne aka fara gudanar da ayyukan kayata hubaren Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf, domin zagayowar lokacin tunawa da idin ghadir, inda aka saka tutoci masu launin kore a koina a ciki da wajen hubbaren.
Ranar 18 ga watan Zulhijjah dai ita ce ranar da manzon Allah ya ayyana Imam Ali (AS) a matsayin magajinsa a bayansa bisa ingantattun ruwayoyi daga bangarorin sunnah da shi’a, wanda kuma wannan ranar tana masayin ranar da mabiya ahlul bait suke tunawa da ita.
A ranar Ghadir mabiya ahlul bait suna yin farin ciki da abin da ya faru na ayyana jagoran ahlul bait (AS) a matsayin magajin manzon Allah (SAW) a bayansa, wanda rana e ta tarihi a addinin muslunci.
A irin wannan rana masoya ahlul bait (AS) sukan taru a hubbaren Imam Ali (AS) domin gudanar da taruka na tunawa da wannan rana.