IQNA

An Kai Hari Kan Jirgin Dakon Man Iran A Kusa Da Jidda Saudiyya

23:05 - October 11, 2019
Lambar Labari: 3484144
Bangaren kasa da kasa, an kai hari da makaman da ake zaton na roka ne a kan jirgin ruwan dakon main a Iran a kusa da Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, farashin mai a duniya ya tashi da kashi biyu cikin dari bayan harin da aka kaiwa wani jirgin dakon man fetur na Iran, da sanyin safiyar yau Juma'a.

Da misalin karfe biyar na safe agogon wurin ne aka jiyo karan fashewar abubuwa guda biyu wadanda ake kyatata zaton harin makamai masu linzami ne kan wani jirgin dakon man fetur na Iran, a kusa da tashar ruwan birnin Jidda na Saudiyya, kan wani jirgin kamfanin man fetur na kasar Iran wanda ya lalata tankar mai guda biyu na jirgin, lamarin ya haddasa malalar man fetur a tekun yankin.

Babu wani abun damuwa dangane da mambobin jirgin da shi kansa jirgin a cewar wata sanarwa da kamfanin man na Iran ya fitar.

tawagar sojojin ruwan Amurka dake Bahrain, ta sanar da cewa ta na da masaniya akan labarin, da kafofin yada labari suak sanar, kan fashewar, amma kawo yanzu ba tada cikakar masaniya kan lamarin.

 

3849010

 

 

 

 

captcha