IQNA

Rauhani: Takunkumin Amurka Kan Iran Laifi Ne Kan Bil Adama

23:55 - October 16, 2019
Lambar Labari: 3484159
Shugaban kasar Iran, Dakta Hassan Rohani, ya bayyana takunkumin Amurka kan kasarsa a matsayin cin zarafin bil adama.

Kamfanin dillancin labaraan iqna, Shugaba Rohani, na bayyana hakan ne yayin taron ministocin kiwan lafiya na kasashen yankin gabashin mediteranien yau Talata a birnin Tehran.
Dama dai shugaban kasar ta Iran ya jima yana kalubalentar takunkumin na Amurka, wanda y ace ta’addanci ne kan tattalin arzikin Iran.
Shugaban kasar ta Iran, ya kuma ce abun kunya ne matakin Amurka na ficewa daga cikin yarjejeniyar kasa da kasa, ta nukiliyar Iran, tare da kakaba wa Iran din takunkumi kan kayan abinci da kuma magunguna.
Ya kara da cewa duk da takunkuman da Amurka ke kakabawa Iran, amma hakan bai sanya Iran ta durkusa a gaban ta ba.
Masana da kamfanonin Iran, sun kara zage datse wajen aiki tukuri domin cike gibin ababen bukatuwa na yau da kulun inji shugaba Ruhanin.

 

3850037

 

captcha