IQNA

Taron Makon Hadin Kan Musulmi Ya Yi Kira Da A Hukunta Kasar Amurka

8:51 - November 16, 2019
Lambar Labari: 3484244
Bayanin bayan taro na makon hadin kan musulmi wanda shi ne karo na 33 ya bukaci ganin an hukunta kasar Amurka saboda yadda take taimakawa kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIL.

Kungiyoyi da jam’iyyun siyasa da su ka fito daga kasashen musulmi daban-daban, wadanda kuma su ke halartar taron na Tehran, sun sha alwashin kai karar Amurka zuwa kotun kasa da kasa ta manyan laifuka domin ta fuskanci shari’a akan kirkiro da goyon bayan kungiyar ‘yan ta’adda da Da’esh da ta yi.

Wasu daga cikin laifukan da masu taron na Tehran suke zargin Amurka da tafkawa sun hada da taimakawa haramtacciyar Kasar Isra’ila akan al’ummar Palasdinu da kuma cutar da al’ummar Yemen ta hanyar yakin da Saudiyya ta shelanta.

Bayanin taron na hadin kan al’ummar musulmi ya kuma nuna cikakken goyon bayansa ga al’ummar Palasdinu da gwagwarmayarsu ta samun ‘yanci, tare da bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Palasdinu.

http://ha.hausatv.com

captcha