IQNA

Wasu Fitattun mata 40 A Duniya Sun Caccaki Isra'ila Kan Shirinta Na Mamaya

22:44 - July 02, 2020
Lambar Labari: 3484944
Tehran (IQNA) wasu fitattun mata a duniya su 40 sun yi watsi da shirin Isra'ila na mamaye yankunan Falastinawa.

Matan su 40 da su ka fito daga bangarori daban-daban na duniya sun bayyana cewa; Daukar mataki irin wannan yana tattare da mummunan sakamako.

A cikin wani bayani da matan su ka fitar sun ci gaba da cewa; Matakin zai rusa kokarin da aka dauki rabin karni ana yinsa domin shimfida zaman lafiya.

Matan wadanda mafi yawancinsu masu fafutuka ne a fagen siyasa, sun kara da cewa; Sun sami sakwanni daga matan Palasdinawa da Isra’ila, da suke jaddada muhimmancin zaman lafiya.

Daga cikin matan da su ka rattaba hannu akan takardar da akwai tsohuwar shugabar kasar Swisland Micheline Calmy-Rey sai tsohuwar shugabar kasar Filland Tarja Kaarina Halonen. Bugu da kari wasu fitattun matan da su ka rattaba hannu akan takardar sun hada da tsohuwar shugabar kasar Kyrgyzia, Roza Utanbayifa, sai tshohuwar shugabar hukumar kare dan’adam ta MDD, Mary Rabinson, da kuma tsohuwar ministar shari’a ta kasar Faransa.

 

3908190

 

captcha