An gina Taj Mahal ne a cikin yankin Gurgan ta India, bayan da sarkin Gurgan ya bayar da umarnin gina wannan wuri, wanda yake hada dukkanin musulmi na Sunnah da shi’a, tare da gudanar da lamurra na addini a cikin ‘yan uwantaka da kaunar juna.
Sarkin wanda yake auren wata mata ba’iraniya, ya sanya an bizne ta a wurin bayan rasuwarta, kamar yadda shi ma aka bizne shi a wurin.
An fara ginin wurin dai tuna cikin shekara ta 1632, an kuma kamala ginin a cikin shekara ta 1647, sannan hukumar raya al’adu da tarihi ta majalisar dinkin duniya ta sanya wannan wuria cikin wuraren tarihi na duniya a shekara ta 1983.
An yi amfani da fasahar gini irin ta Iraniyawa da kuma ta mutanen yankin Gurgan na India wajen gina wannan wuri mai ban sha’awa.