IQNA

Jawabin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Kan Ranar Quds Ta Duniya

20:52 - May 07, 2021
Lambar Labari: 3485887
Tehran (IQNA) a yau ne jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da jawabi kan ranar Quds ta duniya, za a iya karanta cikakken matanin jawabin a kasa

Da Sunan Allah mai rahma Mai Jin Kai

Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu cikamakin annabwa, mafificin halitta baki daya, da alayensa tsarkaka, da kuma sahabbansa zabbabbu da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Falastnu, rayayyen batu mafi muhmmanci na al’ummar Musulmi

Batun Falastinu shi ne batu rayayye mafi muhimmanci da ya hada al’ummar musulmi baki daya. Siyasar tsarin zalunci na jari hujja masu zubar da jini ne da suka samu al’umma a cikin gidanta, a kasarta kasar iyayenta da kakanninta, suka danne su, suka kafa wani gwamnatin ta’addanci ta wasu wadanda ba ‘yan asalin kasa ba.

Manufar tunanin kafa Haramtaccyar kasar Isra’ia

Mece ce babbar manufar kafa haramtacciyar kasar Isra’la? Bisa ga abin da kasashen turai suke rayawa, cewa an zalunci yahudawa a yakin duniya na biyu, saboda haka dole ne a dauki fansa ta hanyar mayar da wata al’umma ‘yan gudun hijira da yi musu kisan kiyashi a yammacin Asia..!

Fito na fito da Haramtaccyar kasar Isra’ia aiki ne kowa da kowa

Wannan shi ne tunanin turawa da yasa suke bayar da goyon bayan baya da kariya ido rufe ga haramtacciyar kasar Isra’ila, sun yi watsi da duk wani ikirarin Demukradiyya da kare hakkin bil adama da suke yi. Sama da shekaru saba’in suna ci gaba da yada wannan ikirari na ban dariya kuma abin da ke sanya kuka, kuma abin ma yana ci gaba da karuwa.

Yahudawan Sahyuniya sun kwace Falastinu bisa zalunci, tun daga ranar farko sun mayar da ita ta zama wani sansani na zalunci. Isra’ila ba kasa ba ce wani sansani ne kawai na ta’addanci akan al’ummar Falastinu da sauran al’ummomin musulmi. Saboda haka fito na fito da wannan haramtacciyar kasa mai zubar da jinni , fito na fito ne da zalunci da kuma ta’addanci, wannan aiki ne da ya rataya a kan kowa.

Rauni da kuma rarrabuwar kawunan musulmi, shi ya haifar da mamaye Falastinu

Wani mai daukar hankali shi ne, duk da cewa an kafa wannan haramtacciyar kasa ne a shekara ta 1948, amma shekaru kafin wannan lokacin sun yi shirin yin hakan a wannan yanki na musulmi. Wadannan shekaru sun yi daidai da lokacin da trawa suka yi kutse a cikin kasashen musulmi ne domin tabbatar da tsarin da babu ruwansa da addini, da kuma ‘yan kasanci na ido rufe, da kuma dora wasu gwamnatoci na kama karya, wadanda za su rika aiwatar da manufofin kasashen turai. Idan aka yi la’akari da abubuwan da suka faru a wadancan shekaruna kasashen Iran, Turkiya, kasashen larabawan yankin yammacin Asia har zuwa arewacin Afirka, to za a ga wannan lamari a zahiri, wanda yake nuna rauni da rarrabuwar kan al’ummar musulmi, shi ne ya bayar da dama har aka mamaye Falastinu, kasashe masu girman kai sun ya haifar da babbar matsala ga duniyar musulmi.

Kasashen Yamma Da Na Gabashin Duniya Sun Hade Baki Akan Yadda Za A kwace Palasdinu

Wani abu mai jan hankali da ya faru a wancan lokacin shi ne yadda bangarorin ‘yan jari hujja da ‘yan gurguzu su ka hade baki da masu kudin ‘yan shayoniya. Birtaniya ce ummul haba’isin kista makarkashiyar, su kuma masu kudin sahayoniya su ka aiwatar da ita da kudaden nasu da kuma makamai. Tarayyar Soviet tana cikin gwamnatoci na farko-farkon da suka yi furuci da kafuwar wannan haramtacciyar gwamnatin, sannan kuma a karshe ta aike da adadin mai yawa na Yahudawa zuwa wancan wurin.

A hakikanin gaskiya, kafuwar tsarin mamaya sakamako ne na yanayin da duniyar musulmi ta kasance a wancan lokacin a gefe daya, sannan kuma a daya gefen, makarkashiya da turawa, ‘yan mamata da kuma azzalumai su ka kitsa.

 A Halin Yanzu An Shiga Wani Yanayi Wanda Duniyar Musulmi Za Ta Amfana

Yanayin da aka shiga a duniya a yanzu, ya sha banban da yadda ake a baya, don haka wajibi ne mu fahimci cewa a wannan lokacin, yanayi ya sauya ta yadda duniyar musulmi za ta amfana. Abubuwan da suke faruwa ta fuskokin siyasa, yanayin zamantakewa a cikin turai da Amurka, raunin da suke da shi da matsaloli masu zurfi, rashin iya tafiyar da al’amurra, da rashin tarbiyya sun fito fili a idon duniya.

Abubuwan da su ka faru a yayin zaben Amurka da gajiyawar masu tafiyar da al’amurra a wannan kasa, da rashin samun nasarar fada da annoba a wannan kasa har na tsawon shekara guda a Amurka da turai, haka nan kuma da rikice-rikicen siyasa da na zamantakewa na bayan nan da suka bayyana a cikin kasashen turai, dukkanin wadannan abubuwan suna a matsyain alamomi ne na koma bayada - kama hanyar –durkushewar turai.

A daya gefen kuwa, kawancen gwagwarmaya yana kara bunkasa a cikin yanki mafi muhimmanci na duniyar musulunci, bunsakar karfinsu na kare kai da kuma kaifarmaki, karuwar fatan da al’ummar musulmi su ke da shi, da karuwar komawa ga musulunci da riko da kur’an, da kuma bunkasa ilimi da son zama masu cin gashin kai,haka nan kuma yadda al’umma take kara dogaro da kanta, dukkannin wadannan suna nuni ne da cewa rayuwa ta gaba za ta yi kyau.

Wajabcin Yadda Kasashen Musulmi Su Hada Kai Da Juna Akan Batun Palasdinu

A karkashin wannan rayuwa mai albarka da take tafe, wajibi ne ga kasashen musulmi su yi aiki tare da juna da hakan zai zama manufa ta tushe, kuma ga dukkanin alamu hakan za ta faru ba da jimawa ba. Wannan hadin kai din da aiki tare ya zamana an yi ne akan batunPalasdinu, da kuma makomar birdin Kudus mai alfarma. Wannan ita ce hakikar da ta kasance a tare da marigayi Imam Khumain ( r.a), ya ayyana ranar juma’ar karshe ta watan Ramadan, a matsayin ranar Kudus ta duniya.

Hadin kai da aiki tare a tsakanin musulmi dangane da birnin kudus mai alfarma, wani a matsayin mummunan mafarki a wurin ‘yan sahayoniya da masu mara musu baya, Amurka da turai.

Shelanta cewa yarjejeniyar karni ta ci kasa, sannan kuma da kokarin kulla alaka da kasashen larabawa masu rauni da ‘yan mamaya, wani yunkuri ne na gujewa mugun mafarki.

Gaba gadi nake cewa; Wannan kokarin ma babu inda zai kai su. Gangarowar da makiya ‘yan sahayoniya su ka fara yi ba za ta tsaya ba, har sai sun iso kasa, don babu abinda zai tare su.

Ababen da suke tabbatar da makoma mai kyau: Ci gaba da gwagwarmaya a yankunan da aka mamaye da kuma goya wa mujahidan Palastinawa baya daga duniyar musulmi

Akwai wasu abubuwa muhimmai guda biyu masu ayyana makoma mai kyau: na farko – kuma mafi muhimmanci – ci gaba da gwagwarmaya a cikin yankunan Palastinu da aka mamaye da kuma karfafa tafarkin jihadi da shahada. Na biyu kuma shi ne goyon bayan gwamnatoci da al'ummar musulmi na duniya ga mujahidan Palastinawa.

Kowa da kowa – 'yan siyasa, masana, malaman addini, jam'iyyu da kungiyoyi, matasa masu kishi da sauran bangarori na al'umma – wajibi ne su tabbatar da matsayarsu cikin wannan yunkuri n agama-gari kana kuma su ba da tasu gudummawar. Wannan shi ne abin da zai kawo karshen makircin makiya wannan kuma shi ne alkawarin Allah na cewa: "Shin suna nufin wani kaidi ne? To wadanda suka kafirta su ne wadanda ake yi wa kaidi", wanda yana nuni misdakin karshen zamani cewa "Kuma Allah ne Marinjayi a kan al'amarinsa, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba".

Ina so in dan ce wani abu ga matasan larabawa da yarensu:

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

Amincin ya tabbata ga dukkanin ma'abota 'yanci na kasashen larabawa, musamman ma matasa. Haka nan aminci ya tabbata ga Palastinawa ma'abota gwagwarmaya da Kudus da masu tsayin daka a masallacin Al-Aqsah.

Aminci ya tabbata ga shahidan gwagwarmaya da sauran mujahidai da suka sadaukar da rayukansu a bisa wannan tafarkin; musamman shahid Sheikh Ahmad Yasin da shahid Sayyid Abbas Musawi, da shahid Fathi Shiqaqi da shahid Emad Mughniyya da Shahid Abdul'aziz Rantisi da Shahid Abu Mahdi al-Muhandis sannan kuma babban shahidin nan na gwagwarmaya, shahid Qasim Sulaimani, wanda kowane guda daga cikinsu bayan rayuwa mai cike da hidima da kuma albarka, haka nan shahadarsa ma ta zamanto mai tasirin gaske cikin tafarkin gwagwarmaya.

Gwagwarmaya Palastinawa da jinin shahidan gwagwarmaya mai tsarki sun sami nasarar dagawa da kuma rike wannan tuta mai albarka sannan kuma suka kara wa Palastinawa irin karfin jihadi da suke da shi ninkin ba ninkiya. A wani lokaci a baya matasan Palastinawa sun kasance suna amfani da duwatsu ne wajen kare kansu, amma a halin yanzu suna mayar da martani ga makiya ne da makamai masu linzami.

Alkur'ani mai girma ya ambaci Palastinu da Qudus a matsayin 'wajaje masu tsarki'; shekaru aru-aru kenan wannan kasa mai tsarki take karkashin mamayar mafiya dauda da lalacewar bil'adama; shaidanun da suke zubar da jinin madaukakan mutane sannan kuma a fili suke bayyanar da hakan da kuma daukan alhakin hakan. Sama da shekaru saba'in kenan wadannan lalatattun mutane suke zubar da jinin ma'abota wannan kasar, yin watandan dukiyarsu kama su da kuma tsare su cikin mawuyacin hali da kuma azabtar da su, amma alhamdu lillahi sun gaza wajen raunana iradar wadannan mutanen (Palastinawa).

Palastinu tana raye kuma za ta ci gaba da jihadin da take yi kuma bisa taimakon Allah za ta yi nasara a kan lalatattun makiyanta. Qudus mai tsarki da dukkanin kasar Palastinu ta Palastinawa ce, kuma lalle za ta koma hannunsu, da yardar Allah, "kuma lalle wannan ba aiki ne mai wahala ba a wajen Allah".

Dangane da lamarin Palastinu dukkanin gwamnatoci da al'ummomin musulmi suna da wani nauyi a wuyansu kuma za a tambaye su, to amma asalin tushen wannan gwagwarmayar su ne al'ummar Palastinun wanda a yau a ciki da wajen kasar sun kai kimanin mutane miliyan sha hudu. Hadin kai da azamar wannan mutanen ne zai iya aiwatar da wani babban aiki. A halin yanzu hadin kai shi ne babban makamin al'ummar Palastinu.

Masu kiyayya da hadin kan Palastinawa su ne gwamnatin sahyoniyawa da Amurka da wasu masu karfi na siyasa na duniya, to sai dai matukar Palastinawan suka hada kansu a cikin gida, to kuwa makiya na waje ba za su iya aikata wani abu ba. Tushen wannan hadin kai wajibi ne ya zama shi ne jihadi na cikin gida da kuma rashin dogaro da makiya. Bai kamata Palastinawa su mai da makiyansu na asali, wato Amurka da Ingila da sahyoniyawa lalatattu, abin dogaronsu na siyasa ba.

Palastinawa – shin wadanda suke Gaza ne ko kuma wadanda suke Qudus da Yammacin Kogin Jordan, ko kuma wadanda suke yankunan 1948 kai hatta ma wadanda suke sansanonin 'yan gudun hijira – su din nan abu guda ne sannan kuma wajibi ne su tsara wani tsari guda, wajibi ne kowane bangare ya goyi bayan daya bangaren da kuma ba shi kariya.

Fatan samun nasara a yau ya fi na kowane lokacin da ya gaba; izanin karfi yana bangaren Palastinawa ne, lalle an samu gagarumin sauyi, sahyoniyawa makiya a kullum sai kara rauni suke yi; sojojinsu wadanda da suke kiran kansu da sunan 'sojojin da ba a iya musu', a halin yanzu bayan abin da ya faru na yakin kwanaki 33 a Labanon da kuma yakukuwan kwanaki 22 da kwanaki 8 a Gaza sun koma su zama 'sojojin da ba za su sake dandanar zakin nasara ba'.

Mummunan yanayi na siyasa da suke ciki da ya sanya su gudanar da zabubbuka guda hudu cikin shekaru biyu, haka nan da mummunan yanayi na tsaro, wanda a kullum sai kashi suke sha sannan da kuma burin da yahudawa suke da shi a kullum na yin hijira da gudu daga wajen, dukkanin wadannan abubuwa ne da suke nuni da tsaka mai wuyan da wannan gwamnatin sahyoniyawan take ciki.

Haka nan kokarin da take yi bisa taimakon Amurka wajen kulla alaka da wasu kasashen larabawa, shi kan sa wata alama ce ta daban da ke nuni da raunin da wannan gwamnati take fuskanta; koda yakehakan ma ba abu ne da zai taimake ta ba. Shekaru aru-aru da suka gabata kenan ta kulla alaka da Masar, tun daga wancan lokacin ya zuwa yanzu gwamnatin sahyoniyawan ta fuskanci shan kashi daban-daban kuma ta kara rauni; a saboda haka shin kulla alaka da wasu 'yan kasashe raunana kuma wulakantattu ne zai taimaka musu? Koda yake su kansu wadannan kasashen babu wani amfani da za su samu daga wannan alakar, sahyoniyawa za su amfana da dukiya da kuma kasarsu ne kawai sannan kuma su yada fasadi da tsarin tsaron a tsakankaninsu.

Tabbas bai kamata wadannan hakikar su kawar da sauran nauyin da ke wuyan mu dangane da wannan yunkurin ba; wajibi ne malaman musulmi da na kirista su haramta kulla alaka da (Isra'ila) sannan su kuma masana da sauran ma'abota 'yanci su yi wa sauran al'umma bayani da sharhi kan mummunan sakamakon hakan ga Palastinu.

A daya bangaren kuma a daidai lokacin da sahyoniyawa suke ta fuskantar rauni da shan kashi, a daya bangaren kuma irin kara samun karfin da sansanin gwagwarmaya yake yi wata bushara ce ga makoma mai kyau: kara samun karfin kare kai da kuma na soji, dogaro da kai wajen samar da makamai masu tasirin gaske, yarda da kai da mujahidai suke da shi, ci gaba da samun wayewa da matasa suke yi, fadaduwar da'irar gwagwarmaya a duk kasar Palastinu hatta ma har da wajen ta, farkawa da kuma yunkurin baya-bayan nan na matasa wajen kare Masallacin al-Aqsah da kuma irin fahimta da kuma yaduwar tunanin gwagwarmaya da kuma fahimtar irin mummunan halin da al'ummar Palastinu suke ciki a tsakanin mafi yawa daga cikin al'ummomin duniya.

Tunani da mahangar Jamhuriyar Musulunci dangane da gwagwarmayar Palastinawa ya samu matsaya a Majalisar Dinkin Duniya, wanda wata mahanga ce mai daukar hankali kuma mai kyau; wato 'yan gwagwarmayar Palastinawa za su iya gabatar da shawarar gudanar da kuri'ar jin ra'ayin dukkanin asalin Palastinawa. Wannan kuri'ar jin ra'ayi kuwa shi ne zai ayyana tsarin siyasa na kasar, sannan kuma dukkanin 'yan asalin kasar ne daga dukkanin kabilu da mabiya addinai ciki kuwa har da Palastinawa 'yan gudun hijira duk za su shiga cikinsa; wannan tsarin siyasar zai dawo da Palastinawa 'yan gudun hijira zuwa gida sannan kuma shi ne zai ayyana makomar bakin haure 'yan share guri zauna.

Wannan tsarin yayi daidai da tsarin demokradiyya da aka sani wanda duniya ta amince da shi kuma babu wani da ya isa yayi kafar ungulu ga hakan. Wajibi ne Palastinawa su ci gaba da wannan gwagwarmaya tasu halaltacciya ta tinkarar sahyoniyawa 'yan share guri zauna ta yadda hakan zai tilasta musu amincewa da wannan mahangar.

Da sunan Allah, su ci gaba da wannan yunkuri na su sannan kuma su san cewa ko shakka babu 'Allah Zai taimaki wadanda suka taimaki addininsa'

 

Wassalamu alaikum wa rahamatullah.

 

3969852

 

 

captcha