IQNA

Firayi Ministar Bangaladesh Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren Isra'ila A Kan Falastinawa

23:51 - May 12, 2021
Lambar Labari: 3485909
Tehran (IQNA) Firayi ministar kasar Bangaladesh ta yi Allawadai da hare-haren Isra'ila a kan al'ummar Falastinu.

Tashar talabijin ta UNB ta bayar da rahoton cewa, a cikin wata wasika da ta aike wa shugaban Falastinawa Mahmud Abbas, Firayi ministar kasar Bangaladesh Sheikh Husaina ta bayyana matsayin kasarta dangane da cin zalun da Isra'ila take a kan al'ummar Falastinu.

Ta ce abin da yake faruwa na kai hare-haren da Isra'ila take yi a kan al'ummar Falastinu abin yin tir da Allawadai ne.

Haka nan kuma ta jaddada cewa a kowane lokaci kasar Bangaladesh da al'ummarta za su ci gaba da kasancewa tare da al'ummar Falastinu.

Sannan ta kirayi kasashen duniya da su sauke nauyin da ya rataya  a kansu an ganin sun taka wa Isra'ila burki dangane da kisan kiyashin da take kan al'ummar Falastinu.

Baya ga haka kuma ta yi kira da a gaggauta samar da hanya wadda za ta baiwa falastinawa damar kafa kasarsu mai cin gishin kanta.

 

 

3971315

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar Bangaladesh
captcha