IQNA

Sheikhul Azhar Ya Aike Da Sakonni A Cikin Harsuna 15 Domin Taimakon Falastinawa

23:50 - May 15, 2021
1
Lambar Labari: 3485916
Tehran (IQNA) Babban Shehun Azhar ya kirayi al'ummomin duniya da su taimaka ma al'ummar Falastinu.

Babban Shehun Azhar din Dr. Ahmad Tayyib, ya wallafa sako a shafinsa na “Facebok” da harsunan duniya 15 ya bayyana cewa; Ina yi kira ga al’ummun duniya da shugabanninsu da su taimakawa al’ummar Palasdinu wanda aka zalunta, saboda su sake kwato hakkokinsu da kasarsu da wurarensu masu tsarki

Dr. Sheikh Ahmad Tayyib ya kuma ci gaba da cewa; Ku yi kokarin tsayar da kisan da ake yi wa Palasdinawa, ku taimaki masu gaskiya.

Babban malamin na jami’ar Azrhar ya karkare sakon nasa da rokon Allah da ya yi rahama ga shahidan Palasdinawa, ya kuma lullube su da rahama.

Kwanaki kadan da su ka gabata ma dai shugaban jami’ar ta Azhar ya bayyana cewa; Ko badade ko bajima Haramtacciyar Kasar Isra’ila za ta rushe.

 

 

3971562

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
allah yajikan musulmi
captcha