IQNA

Sanatan Amurka Bernie Sanders Ya Yi Allawadai Da Matsananciyar Akidar Sahyuniyanci Ta Netanyahu

23:56 - May 15, 2021
Lambar Labari: 3485918
Tehran (IQNA) Dan majalisar dattijan Amurka Bernie Sanders ya yi tir da irin tsatsauran ra'ayin Netanyahu.

Shafin Yahhoo News ya bayar da rahoton cewa, Dan majalisar dattijan na Amurka Bernie Sanders ya bayyana cewa, irin matsananciyar akidar Netanyahu ce ta kara sanya lamurra suka tsanata a wanann lokaci da kowa ke son zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

Ya ci gaba da cewa a kowace shekara gwamnatin Amurka tana ware dala biliyan 4 da take bai wa Isra'ila a matsayin taimako, ya ce bai kamata wanann taimakon ya zama karkashin gwamnati irin ta Netanyahu ba, dole ne Amurka ta canja salo.

Ya ce kamar yadda Isra'ila take ad hakki ta kare kanta, haka nan kuma su ma Falastinawa suna da hakki na rayuwa kamar kowane dan adam, kuma rayuwarsu tana da muhimmanci kamar kowa.

Sanders ya ce, idan irin wannan siyasar ta neman tashin hankali da rashin son zaman lafiya ta Netanyahu ta ci gaba da tafiyar da Isra'ila, to kuwa hadarin da zai biyo bayan hakan zai shafi ita kanta Amurka, da dukkanin kasashen turai da kuma latin Amurka.

 

3971571

 

captcha