Fitaccen makarancin kur'ani dan kasar Iran Hamed Shaker Najad a lokacin da yake gabatar da karatun kur'ani mai tsarki a cikin watan Ramadan mai alfarma na shekara ta 2019 a birnin Hamburg na kasar Jamus.
An haifi Hamed Shaker Najad a birnin Mashhad na kasar Iran, amma ya halarci kasashen duniya da dama domin gudanar da karatun kur'ani, kamar yadda kuma a shekarun baya ya sha lashe gasar kur'ani ta duniya a lokuta daban-daban.