Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce za su ci gaba da kai hare-hare kan al'ummar zirin Gaza har nan da wasu kwanaki masu zuwa.
Jaridar Times ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da Netanyahu yake ganawa da wasu daga cikin magaddan gari daga wasu yankunan kudancin Falastinu da Isra'ila ta mamaye, ya bayyana cewa za su ci gaba da kai hare-hare kan al'ummar zirin Gaza har nan da wasu kwanaki masu zuwa., bayan nan kuma duk wani da za a kai kansu za su mayar da martani mai tsanani.
Tun bayan da aka kafa haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin kasar Falastinu, ba ta taba fuskantar turjiyar da ta fuskanta da hare-haren ramuwar gayya kamar irin wannan lokacin ba.
Duk da kisan Falastinawa kananan yara da mata da tsoffi da sauran fararen hula da Isra'ila take yia Gaza, amma a wannan karon lamarin ya sha banbam da sauran shekarun baya, domin a wannan karon ta fuskanci martani da makamai masu linzami sama da dubu uku a cikin kasa da mako guda daga Falastinawa.
Hare-haren martanin na Falastinawa ya jawowa Isra'ila asarori masu tarin yawa na tattalin arziki, baya ga halakar wasu yahudawa da suka hada har da jami'an tsaronta, baya ga haka kuma a wanann karon dukkanin yankunan Falastinawa ne talke fuskantar turjiya ba a Gaza ba kawai, ida koa yau Lahadi a cikin yankunan gabar yamma da kogin Joradan, Falastinawa sun halaka wasu yahudawa biyu ta hanyar harbe su da bindiga a musayar wuta da suka yi da su.