IQNA

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya ce:

Masu kai wa Yemen hari sun kasa cimma manufofinsu

15:31 - September 20, 2022
Lambar Labari: 3487885
Tehran (IQNA) Yayin da yake ishara da shigar da Amurkawa da Saudiyya suka yi a wannan kasa, jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yaman ya ce: Idan har kawancen 'yan ta'adda ya mamaye sauran yankuna, to za su yi abin da ya fi wannan muni, amma duk da kokarin da suke yi, sun kasa cimma burinsu.

Jagoran Kungiyar Ansarullah da aka fi sani da Alhuthi a kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Badruddin Alhuthi ya bayyana cewa, babbar manufar amurka  a kasar Yemen ita ce mamaye kasar, ko kuma haifar da tashe-tashen hankula a tsakanin al’ummominta.

Alhuthi ya bayyana hakan ne a  yau a cikin wani jawabi wanda ya gabatar da aka watsa kai tsaye  a kafofin yada labaran kasar Yemen.

Ya ce tun kafin wannan lokacin Amurka ta yi ta hankoron ganin ta haifar da matsaloli a  Yemen, wanda hakan zai bata damar mamaye kasar cikin sauki, amma hakan bata samu, sakamakon tsayin daka al’ummar kasar suka yi.

Ya ci gaba da cewa, gazawar Amurka ce ta sanya ta yin amfani da akrnukan farautarta na yankin, domin su aiwatar da manufofinta na ruguza kasar Yemen

Ya yi ishara day akin da Saudiyya take kaddamarwa a kan al’ummar kasar yemen tsawon shekaru fiye da bakawai a jere da cewa, aiwatar da shirin Amurka ne, kuma har yanzu wannan manufa bata tabbata ba, domin kuwa bayan kwashe tsawon wadannan shekaru an kisan kiyashi da ragarza masallatai da kasuwanni da asibitoci, da cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu, har yanzu al’ummar Yemen ba su mika kai ga manufofin ‘yan mamaya ba.

Tun a cikin shekara ta dubu biyu da sha biyar ne Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare kan al’ummar kasar Yemen da nufin rusa kungiyar Alhuthi wadanda suke yi mata taurin kai da kin mika wuya ga manufofinta  a cikin kasar Yemen.

Duk da cikakken goyon bayan da Saudiyya take samu daga gwamnatocin kasashen turai musamman Amurka da Burtaniya da Faransa, da kuma muggan makaman da take sayea  wurinsu domin yin amfani das u kan al’ummar yemen, amma har yanzu audiyay ba ta iya cimma ko daya daga cikin manufifinta na yakin ba.

 

4086906

 

 

 

captcha