IQNA

‘Yar kasar Morocco, alƙaliya ta farko da lulluɓi a kotunan Italiya

15:28 - January 17, 2023
Lambar Labari: 3488517
Tehran (IQNA) An nada wata mace 'yar Morocco a matsayin alkaliya ta da lullibi  a kotunan Italiya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press Bay cewa, Hajar Boudraa, ‘yar shekaru 30 ‘yar kasar Moroko, ‘ amatsayin alkali na farko da lullubi a kasar Italiya bayan ta ci jarrabawar kammala karatun jami’ar shari’a ta Turin.

Zaben da aka yi wa Mrs. Boudra a matsayin alkali musulma ta farko a Italiya ya ja hankalin jaridun kasar. A cewar abin da aka fada a wadannan kafafen yada labarai, ita diyar wani manomi dan kasar Morocco ne da ke aiki a gonaki da ke arewacin Italiya.

A halin yanzu Hajar Bodraa tana aiki a matsayin mai horarwa a sashin gabatar da kara na kotun Verona kuma tana kammala kwasa-kwasan horar da shari'a.

A cikin kalamanta ta ce an haife ta  ne a kasar Maroko sannan ta yi hijira tare da iyalansa zuwa kasar Italiya da birnin Verona, inda mahaifinsa yake aikin noma.

 

4115148

 

Abubuwan Da Ya Shafa: aikin noma Maroko kotu italiya alkaliya
captcha