IQNA

Karatun Qari na Masar a tsakanin Musulman Afrika

Tehran (IQNA) Abdul Naser Harak, wani makaranci dan kasar Masar, ya karanta ayoyin kur'ani a gaban musulmin tsibirin "Mayotte" na Afirka.

A matsayinsa na makarancin kur'ani kuma alkali na duniya, Sheikh Abdul Nasser Harak ya zagaya kasashe sama da 43, kuma yana da masoya da dama a duk fadin duniya saboda kwarewar karatun kur'ani. Da yawa suna kiransa Malamin Karatu a wurare daban-daban da kuma sabon Gloosh, saboda yana kwaikwayi salon karatun wannan babban Malami sosai.