IQNA

Mahukuntan BIrnin Paris Za su Kai Karar Tashar Fax News

22:45 - January 21, 2015
Lambar Labari: 2742218
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan birnin Paris na kasar Faransa na shirin kai karar tashar Fax News ta kasar Amurka saboda cin zarafin musulmin Faransa tare da yin karyar cewa an hana su shiga wani bangare na birnin.

Kamfanin dillancin labaran Inqa ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Lepiot cewa a jiya mahukuntan birnin Paris na kasar Faransa sun sanar cewa suna shirin shigar da kara kan tashar Fax News ta kasar Amurka wadda ta watsa shirin cin zarafin musulmin kasar Faransa tare da yin karyar cewa mahukuintan birnin sun hana su shiga wani bangare nasa saboda dalilai na ta’addanci.
Bayanin y ace bayar da hakuri da tashar ta Fax News ta yi bai wadatar ba, domin kuwa ta ci mutuncin al’ummar birnin Paris ta hanyar yi musu kage, da kuma kokarin haifar da fitina da tashin jituwa a tsakanin mazauna birnin da suke bin addinai mabanbanta a tare da wata matsala  atsakaninsu ba.
A cikin makon nan ne dai tashar ta gayyaci wani mai mata sharhi wanda ya yi kalamai na batunci da kokarin jawo kiyya ga musulmi, ta shara karya a kan cewa an hana musulmi shiga wani bangare na birnin Paris, sakamkon hare-haren da wasu musulmi suka kai a birnin, inda ya yi ta kokarin danganta ayyukan ta’addanci da addinin muslunci.
Da dama daa cikin al’ummomi9n faransa sun nuna rashin jin dadinsu da wannan shiri da tashar ta watsa, wanda kuma wata kila hakan shi ne dalilin da yasa mahukuntan suka dauki wannan mataki gurfanar da tashar a gaban kuliya.
2738864

Abubuwan Da Ya Shafa: paris
captcha