IQNA

An Raba Kur’ani Da Furanni A Paris Domin Maida Martani Kan Kyamar Musulunci

12:46 - January 29, 2015
Lambar Labari: 2778865
Bangaren kasa da kasa, a wani mataki na mayar da martani kan abin da jaridar Charlie Hebdo ta yin a batunci ga addinin muslunci musulmi sun raba kur’ani mai tsarki da furanni a birnin Paris ga jama’a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almisriyun cewa, musulmi sun raba kur’ani mai tsarki da furanni a birnin Paris ga jama’a mayar da martani kan abin da jaridar Charlie Hebdo ta yin a batunci ga manzon Allah (SAW) da jaridar ta yi.
Sakamakon abin da wannan jarida ta yi ya jawo fushin musulmi a koina cikin duniya, inda jami’ai cibiyoyi dalibai ‘yan kasuwa da sauran al’ummar jamhuriyar muslunci suka ci gaba da Allah wadai da mujallar kasar Faransa Charlie Hebdo sakamakon batancin da ta yi wa Manzon Allah.

Rahotannin sun ce dubun dubatan al’ummar kasar din ne suka taru a masallatan jam'i a duk fadin kasar ta Iran da suka hada da garuruwan don yin tofin Allah tsine ga mujallar.
Haka nan kuma wasu rahotannin sun ce daga cikin abubuwan da aka gudanar a yayin wadannan tarurruka har da sallar jam'i, karatun Alkur’ani mai girma bugu da kari kan lakcoci dangane da matsayin Manzon Allah da kuma tona asirin irin makirce-makircen makiya a kokarinsu na sanya kyamar Musulunci da musulmi cikin zukatan al’ummomin kasashen yammaci.
A sauran kasashen musulmi ma dai ana ci gaba da gudanar da tarurruka da jerin gwanon rashin amincewa da wannan danyen aikin da mujallar kasar Faransan ta yi da kuma ci gaba da goyon bayanta da gwamnatocin kasashen yammacin suke yi.
2774731

Abubuwan Da Ya Shafa: paris
captcha