IQNA

Ana Nuna Goyon Baya Ga Sheikh Zakzaky A Tarukan Maulidin Manzo (SAW)

23:43 - December 13, 2016
Lambar Labari: 3481031
Bangaren kasa da kasa, a daiai lokacin da ake gudanar da tarukan maulidin amnzon Allaha kasashe daban-daban an Afirka da kuma Keshmir, an nuna goyon baya ga sheikh Zakzaky.
Ana Nuna Goyon Baya Ga Sheikh Zakzaky A Tarukan Maulidin Manzo (SAW)

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a lokacin da ake gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW) a kasashen Afikra da kuma cikin Najeriya kamar a Katsina, sai kuma a Keshmir, an nuna goyon baya ga sheikh Zakzaky, jagoran harkar muslunci a Najeriya.

Masu gudanar da taruka da kuma jerin gwanon sun rika daga totocin sheikh Zakzaky, suna masu kira ga mahukuntan Najeriya da su sake daga tsare da suke yi tare da mai dakinsa.

Tun a cikin watan Disamban da ya gabata ne jami’an sojin Najeriya suka kaddamar da farmaki da makamai a kan gidan sheikh Zakzaky da ke Zaria, inda suka kashe mutane da dama, da suka hada da Sheikh Muhammad Turi, da kuma Dr. Musatafa said.

A nata bangaren gwamnatin jahar Kaduna ta tabbatar da cewa sojoji sun bizne gawwakin yan shi’a da suka kasha a cikin rami guda da yawansu ya kai dari uku da arbain da bakwai, amma magoya bayan malamin sun ce adadin wadanda sojoji suka kasha ya hura dubu daya, inda suka fitar da sunayensu.

3553752

captcha