IQNA

Daesh Ta Yi Barazanar Yin Kisan gilla Kan Jama’a A Lokacin Bukuwan Sabuwar Shekara

19:55 - December 30, 2016
Lambar Labari: 3481082
Bangaren kasa da kasa, kungiyar ta’addanci ta Daesh ta yi barazanar cewa za ta yi kisan kiyashi a kan jama’a a kasashe daban-daban a lokacin bukuwan sabuwar shekara.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Sun ta kasar Birtaniya cewa, kungiyar ‘yan ta’addan ISIS sun shirya tsaf domin kaddamar da munanan hare-hare na kisan gilla a kan jama’a a lokutan gudanar da bukukuwan sabuwar shekara.

Rahoton ya ce jami’an tsaron kasar Australia sun damke wani mutum da ya isa kasar daga birnin Landan na kasar Birtaniya, wanda ta bayyana cewa mamba ne na kungiyar ISIS, ya kuma bayyana cewa ya zo Australia ne kawai domin ya kaddamar da hare-hare a lokacin taron bukukuwan sabuwar shekara a kasar.

Ya kara da cewa baya ga Aistralia, akwai wadanda aka tura zuwa wasu kasashendomin wannan aiki, daga ciki kuwa har da wasu biranen kasashen turai.

Jami’an tsaron kasar ta Australia sun samu nasarar damke mutumin ne bayan samun wasu bayanan sirri daga wasu ‘yan kasar wadanda suka yi shakku kan take-takensa.

An kame wannan dan ta’adda ne dai a Australia, bayan kame wani mutum a birnin Moscow na kasar Rasha, wanda shi ma yake da shirin kaddamar da wasu hare-haren makamanta haka.

3557853


captcha