IQNA

Tattaunawar Musulmi Da Wadanda Ba Musulmi Ba A Tomstown

22:42 - May 02, 2017
Lambar Labari: 3481459
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a birnin Tomstown na jahar Victoria a kasar Australia sun gayyaci sauran mabiya addinai zuwa masallaci domin tattaunawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na starweekly cewa, masallacin Tomstown da ke jahar Victoria na daga cikin masallatai 15 mafi girma akasar Australia.

Babbar manufar wannan shiri mai taken kofofin masallaci a bude shi ne, bayar da dama ga sauran mabiya addinai da su samu masaniya akan addinin muslunci, kasantuwar babu inda za su samu bayani kan muslucni na hakika sai a wurin musulmi.

Muhimmin abin da ke yi dais hi ne, ana tarbar dukkanin mutanen da suka zo wurin tare da girmama su da kuma nuna musu wasu daga cikin abubuwa na muslunci, da suka hada da littafai da kur'ani mai tsarki, tare da amsa musu tambayoyin da suke da su a kan addinin muslunci.

Muhyiddin shi ne limamin wannan masallaci ya kuma bayyana cewa, hakika gudanar da shiri irin wannan yana da bababn tasiri wajen kara karfafa alaka tsakanin musulmi da kuma wadanda ba musulmi, ta yadda za a kawar da kyamar juna da kuma samun fahimta da zaman lafiya.

3595218

captcha