IQNA

Majami’a Na Bayar Da Abincin Buda Baki A Australia

19:45 - June 10, 2017
Lambar Labari: 3481599
Bangaren kasa da kasa, majami’ar birnin Perth na kasar Australia na bayar da buda baki a cikin watan Ramadan mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na IBC cewa, a karon farko majami’ar birnin Perth na Australia ta kirayi buda baki da ya hada musulmi da kiristoci a wuri guda.

Faidil shi ne limamin muuslmi a birnin na Perth ya bayyana cewa, tsawon shekaru shida kenan a jere a kowane watan Ramadan majami’ar birnin tana shiryawa musulmi buda baki, amma a wannan shekara ta shirya buda bakin tare da gayyatar musulmi da kiristoci.

Malamin ya ce hakika wannan lamari ne da ke cike da hikima, domin kuwa awannan lokacin kiyayya da musulmi na kara kamari a tsakanin al’ummomin kasar ta Australia wadanda mafi yawa kiristoci ne, amma shirya irin wannan buda baki zai sanya kiristoci da dama su fahimci yadda musulmi suke da halayensu, sabanin yadda suke tunani.

Hamfres wani kirista da ya musulunta wanda ya halarci wurin, ya bayyana cewa wannan taron buda sai ya kara tabbatar masa da cewa dukkanin ‘yan adam tushensu daya ne, kuma za su iya haduwa a kan wani abu na fahimta da kaunar juna duk da banbancin maganga da ke tsakaninsu.

Aisha Nawakovich wata lauya ce musulma wadda ta halarci wurin, ta bayyana cewa wannan taro zai taimaka matukawajen samar da fahimta da kuma kyamar da wasu ke nuna ma musulmi a Australia.

3607842



captcha