IQNA

An Samu Wani Kur'ani Bai Bace Ba Bayn Kai wani Harin Ta'addanci A Alkahira

23:49 - December 25, 2017
Lambar Labari: 3482235
Bangaren kasa da kasa, an samu wani kwafin dadden kur'ani mai tasrkia  cikin wani gini da 'yan ta'adda suka kai wa hari a Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misrawi cewa, Ahmad Shauki shugaban babban cibiyar da ke kula da adana kayan tarihi na birnin Alkahira ya bayyana cewa, an samu wani kwafin kur'ani mai tsarki ba tare da wani abu ya same shi ba, duk da harin ta'addancin da aka kai wurin.

Ya kara da cewa 'yan ta'addan sun kai harin ta'addanci da bama-bamai a kan ginin cibiyar adana dadaddun kayan tarihin ne da ke birnin Alkahira, inda suka lalata wurin, amma abin mamaki shi ne yadda wannan kur'ani bai kone da wuta ba.

Wata kungiyar 'yan ta'addan wahabiyawa mai suna Ansaru bait Maqdis ce ta dauki nauyin kai wannan harin ta'addanci a kan wannan cibiya ta adana kayan tarihi ta Masar.

3676048

 

 

 

 

captcha