IQNA

Ginin Masallaci Mai Tulluwa 99 Kokari Ne Na Hada Mabiya Addinai A Sydney

22:36 - January 02, 2018
Lambar Labari: 3482262
Bangaren kasa da kasa, ginin masallaci mai tulluwa 99 ya ja hankulan jama'a matuka  akasar Australia yayin da Angelo Candalepas wanda tsara ginin masallacin ya nuna farin cikinsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta CNN ta bayar da rahoton cewa, zaa bude wannan ginin masallaci ne a cikin watan azumi na wannan shekara.

Tun a cikin watan Satumban da ya gabata ne aka bude kofofin wannan masallaci ga jama'a domin su duba su ga yadda ake gudanar da aikinsa.

Da dama daga cikin wadanda suka halarci wadanda mafi yawansu ba msuulmi ba ne, sun nuna mamakin su matuka dangane da yadda aikin ya gudana, inda wasunsu ke cewa bat aba ganin wani wuri na ibada mai da aka gina kamar wannan ba.

Zakariya Matyus shi ne shugaban cibiyar musulmin birnin Sydney, ya bayyana cewa hakika wannan aiki yana daga cikin muhimman lamurra da musulmin kasar suke alfahari da shi.

Wani kuma wanda ya kara bayar da mamaki dangane da sha'anin wannan masallaci shi ne yadda mahukunta a kasar suka bayar da izinin ginin masallacin cikin kankanin lokaci ba tare da bata lokaci ba, wanda hakan bata taba faruwa ba a tarihin musulmin kasar.

3678350

 

 

مسجد 99 گنبدی سیدنی؛ تلاشی برای توسعه روابط بین ادیان

مسجد 99 گنبدی سیدنی؛ تلاشی برای توسعه روابط بین ادیان

مسجد 99 گنبدی سیدنی؛ تلاشی برای توسعه روابط بین ادیان

مسجد 99 گنبدی سیدنی؛ تلاشی برای توسعه روابط بین ادیان

 

 

captcha