IQNA

Majalisar Tsaron Yahuwa Za ta Kada Kuri'a Kan Mamaye Wasu Yankunan Palastinawa

22:55 - January 21, 2018
Lambar Labari: 3482322
Bangaren kasa da kasa, majalisar tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila za ta kada kuri'an amincewa ko akasin hakan kan mamaye wasu yankunan palastinawa.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na safa cewa, majalisar tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila za ta kada kuri'an amincewa ko akasin hakan kan mamaye wasu yankunan palastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan, bisa hujjar cewa akwai matsugunnan yahudawa 'yan kaka gida ke wuraren.

Bayanin ya ci gaba da cewa, an gabatar da wannan daftarin dokar ne ga majalisar tsaron kasa, wanda kuma idan aka amince da shi, haramtacciyar kasar Isra'ila za ta kara fadada yankunan mamayarta a cikin yankunan palasinawa.

Jami'ai Likud ta firayi ministan yahudawan sahyuniya Benjamin Netanyahu ya riga ya amince da haka, kuma ana ganin cewa akasarin magoya bayan jami'ar mambobi a majlaisar tsaron kasa za su amince da wannan daftarin kudiri.

3683892

 

 

 

 

captcha